Deuteronomy 24:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da kuka kakkaɓe ’ya’yan zaitun daga itatuwanku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ كَكَكَّٻٜىٰ یَیَنْ إِتَاثٜىٰنْ ظَيْتُنْ نَاكَ، بَذَاكَ سَاكٜىٰ بِنْ رَسَّنْ كَنَ كَكَّٻٜىٰوَبَ؞ ذَاعَبَرْ وَبَڧِ دَ مَرَايُ دَ مَاتَانْدَ مَذَنْسُ سُكَ مُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da kuka kakkaɓe 'ya'yan zaitunku, kada ku sāke bin rassan kuna kakkaɓewa, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.