Deuteronomy 25:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma fa, in mutum ba ya so yă auri matar ɗan’uwansa, sai tă tafi wurin dattawa a ƙofar gari tă ce, “Ɗan’uwan mijina ya ƙi yă wanzar da sunan ɗan’uwansa a Isra’ila. Ya ƙi yă cika abin da ya kamaci ɗan’uwan miji yă yi gare ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا عِدَنْ طَنْعُوَنْ مِجِنْ بَايَسُواْ يَطَوْكِ مَاتَرْ طَنْعُوَنْسَ دَ يَمُتُ تَذَمَ مَاتَرْسَ، سَيْ مَاتَرْ تَتَڢِے وُرِنْ دَتَّاوَا عَڧُواْڢَرْ غَرِ تَثٜىٰ، ‹طَنْعُوَنْ مِجِنَ يَڧِ يَكَڢَ سُونَنْ طَنْعُوَنْسَ دَ يَمُتُ، يَڧِ يَثِكَ حَكِّنْ طَنْعُوَنْ مِجِ أَغَرٜىٰنِ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan'uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan'uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan'uwansa cikin Isra'ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan'uwan marigayi, ya yi.’