Deuteronomy 26:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ku faɗa wa Ubangiji Allahnku, “Na cire tsattsarkan rabo daga gidana na kuma ba wa Balawe, baƙo, maraya da gwauruwa, bisa ga dukan abin da ka umarta. Ban ja gefe daga umarnanka ko in manta da wani a cikinsu ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً ذَاكُيِ مَغَنَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ كُثٜىٰ، ‹نَارِغَا نَا ڢِتَرْدَ زَكَّرْ دَ عَكَ كٜىٰٻٜىٰ دَ ڟَرْكِے دَغَ ثِكِنْ غِدَانَ، نَا كُمَبَا لَوِيَاوَا دَ بَڧِنْ دَسُكٜىٰ ذَمَ عَثِكِنْمُ دَ مَرَايُ دَ مَاتَانْدَ مَذَنْسُ سُكَ مُتُ بِسَغَ دُكَنْ عُمَرْنِنْدَ كَاعُمَرْثٜىٰنِ؞ بَنْ كُوَ ڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْ مَنْتَادَ وَنِ عُمَرْنِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan za ku ce a gaban Ubangiji Allahnku, ‘Na fitar da tsattsarkan kashi daga cikin gidana na ba Balawe, da baƙo, da maraya, da matar da mijinta ya rasu bisa ga umarnin da ka yi mini. Ban karya wani umarninka ba, ban kuwa manta da su ba.