Deuteronomy 26:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
sai ku ɗauki ’ya’yan fari na dukan amfanin gonar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku zuba a kwando. Sa’an nan ku je wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă zama mazauni don Sunansa,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كُطِبَ دَغَ ثِكِنْ نُونً ڢَارِ نَدُكَنْ أَمْڢَانِنْ ڧَسَا وَنْدَ كُكَ شُوكَ عَڧَسَرْدَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَكٜىٰ بَاكُ؞ كُسَا ثِكِنْ ݣُونْدُواْ كُكَيْ وُرِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ ذَيْ ذَاٻَا دُواْمِنْ عَيِ سُجَّدَ دَ سُونَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
to, sai ku keɓe nunan fari na dukan amfanin ƙasa wanda kuka shuka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Ku sa cikin kwando, ku tafi inda Ubangiji Allahnku zai zaɓa don ya tabbatar da sunansa.