Deuteronomy 29:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, tă koma ga bauta wa gumakan waɗannan al’ummai. Kada a sami wani tushe mai ba da ’ya’ya masu dafi, masu ɗaci a cikinku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُتَبَّتَرْ ثٜىٰوَ بَابُ ذُوثِيَارْ وَنِ مُتُمْ، كُواْ تَوَتَ مَثٜىٰ، كُواْ تَ عِيَلِ، كُواْ تَوَتَ ذُرِيَ عَثِكِنْكُ، وَدَّ ذُوثِيَارْ تَجُويَ غَ بَرِنْ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْمُ دُواْمِنْ تَبَوْتَا وَ أَلُّواْلِنْ وَطَنَّنْ أَلْعُمَّيْ؞ كَدَ ڢَا عَتَرَرْ دَ وَنِ عَثِكِنْكُ مَيْ ذَمَ كَمَرْ تُوشٜىٰنْ ڟِرُواْ مَيْ بَادَ یَیَ مَاسُ دَڢِ، مَاسُ طَاثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al'umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da 'ya'ya masu dafi, masu ɗaci.