Deuteronomy 3:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
(Og sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu cikin Refahiyawa. An yi gadonsa da ƙarfe, tsawon gadon ya fi ƙafa goma sha uku, fāɗinsa kuwa ƙafa shida ne. Yana nan a Rabba ta Ammonawa har yanzu.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے عُواغْ نَ بَشَنْ نٜىٰ كَطَيْ يَضَغٜىٰ دَغَ ذُرِيَرْ ڧَتِّنْ مُتَنٜىٰنْ رٜىٰڢَيَاوَا؞ غَدُوانْسَ نَڧَرْڢٜىٰ نٜىٰ، ڟَوُانْسَ يَڢِ ڧَڢَا غُواْمَشَا عُكُ، ڢَاطِنْسَ كُمَ يَكَيْ ڧَڢَا شِدَ؞ يَنَنً عَثِكِنْ بِرْنِنْ رَبَّهْ تَ أَمُّواْنَاوَا هَرْوَيَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
(Sai Og, Sarkin Bashan, ne kaɗai ya ragu daga cikin Refayawa. Gadonsa na ƙarfe ne. Gadon yana nan a Rabbah ta Ammonawa. Tsawonsa kamu tara, faɗinsa kuma kamu huɗu ne.)