Deuteronomy 3:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Cikin ƙasar da muka kwasa a lokacin, na ba wa mutanen Ruben da mutanen Gad yankin arewa na Arower ta Kwarin Arnon, haɗe da rabin ƙasar tudu ta Gileyad, tare da biranenta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«أَ لُواْكَثِنْ دَ مُكَ ڨُوثٜىٰ وَنَّنْ ڧَسَرْ، نَبَا ذُرِيَرْ رَعُبَيْنُ دَ تَ غَدْ أَبِنْدَ يَطَوْكَ دَغَ يَنْكِنْ أَرُواْوٜىٰرْ وَنْدَ يَكٜىٰ عَبَاكِنْ ݣُورِنْ كُواْغِنْ أَرْنُوانْ، تَرٜىٰدَ رَبِنْ يَنْكِنْ تُدَّيْ نَ غِلٜىٰيَدْ دَ غَرُرُوَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'ad da muka mallaki ƙasar a wannan lokaci, sai na ba Ra'ubainawa da Gadawa yankin ƙasar daga Arower wadda take gefen kwarin kogin Arnon, da rabin ƙasar tuddai ta Gileyad tare da garuruwanta.