Deuteronomy 3:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wannan lokaci muka kwashe dukan biranensa. Babu ɗaya daga birane sittin da ba mu ɗauke daga gare su ba, dukan yankin Argob, masarautar Og a Bashan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُكَثِ دُكَنْ غَرُرُوَنْسَ أَ لُواْكَثِنْ؞ بَابُ كُواْ وُرِے طَيَ مَيْ كَتَنْ‌غَ عَثِكِنْ غَرِ وَنْدَ بَمُكَرْٻَ دَغَ غَرٜىٰشِيبَ؞ دُكَنْ غَرُضُوً دَ مُكَثِ دَ يَاڧِ سُنْ كَيْ سِتِّنْ، وَتُواْ دُكَنْ يَنْكِنْ أَرْغُوابْ دَ دُكَنْ يَنْكِنْ مُلْكٍ عُواغْ نَ بَشَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Muka ƙwace dukan garuruwansa a wannan lokaci. Ko gari guda ɗaya, ba mu bar musu ba, garuruwa sittin, da dukan yankin Argob, da mulkin Og a Bashan.