Deuteronomy 31:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da na kawo su cikin ƙasa mai zub da madara da zuma, ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa ga kakanninsu, sa’ad da kuma suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba, za su juya ga waɗansu alloli su bauta musu, su ƙi ni, su kuma karya alkawarina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَنْ كَٰوُاْسُ ثِكِنْ ڧَسَا مَيْ أَمْڢَانِ وَدَّ نَيِ أَلْڧَوَرِ تَرٜىٰدَ ضَنْڟُوَا ذَنْبَا كَاكَنِّنْسُ؞ سَعَدَّ سُكَثِ سُكَ ڧُواْشِ سُكَيِ ڧِبَ أَوُرِنْ، ذَاسُ جُويَا غَ وَطَنْسُ أَلُّواْلِ سُبَوْتَا مُسُ، سُرٜىٰنَ نِے سُكُمَ كَرْيَ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina.