Deuteronomy 32:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zan aika da yunwa mai tsanani a kansu, zazzaɓi mai zafi da muguwar annoba; zan aika da haƙoran namun jeji a kansu, da dafin mesa masu ja da ciki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يُنْوَ ذَاتَ لَلَتَرْدَسُو، ذَاڢِنْ ثِيوُاْ ذَيْثِنْيٜىٰسُ، مُوغُنْ بَلَعِ ذَيْ هَلَكَاسُ؞ ذَنْ عَيْكَ دَ نَمُواْمِنْ دَاجِ عَكَنْسُ، دَ دَڢِنْ حَلِتُّو مَاسُ رَرَّڢٜىٰ عَڧَسَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su lalace saboda yunwa, Zazzaɓi mai zafi, da muguwar annoba za su cinye su. Zan aika da haƙoran namomi a kansu, Da dafin abubuwa masu jan ciki.