Deuteronomy 32:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma ina tsoron tsokanar abokin gāba, don kada abokan gāba su kāsa ganewa har su ce, ‘Hannunmu ne ya yi nasara; ba Ubangiji ne ya aikata dukan wannan ba.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا إِنَ غُدُنْ ڟُواْكَنَرْ أَبُواْكَنْ غَابَا، غَمَا أَبُواْكَنْ غَابَنْسُ ذَاسُ عِيَ ثٜىٰوَ «دَ حَنُّنْمُ مُكَيِ نَصَرَا، بَ يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ يَيِ وَنَّنْبَ!» ›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma saboda gudun tsokanar maƙiyi, Kada abokan gābansu su zaci su ne suka ci nasara. Ai, ni ne na yi wannan.’