Deuteronomy 33:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Cikin daraja yana yi kamar ɗan fari na bijimi; ƙahoninsa ƙahonin ɓauna ne. Tare da su zai tukwiyi al’ummai, har ma da waɗanda suke ƙarshen duniya. Haka dubu dubban Efraim suke; haka dubban Manasse suke.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَرَجَرْسَ كَمَرْ تَطَنْ ڢَارِ نَبِجِمِ تَكٜىٰ، ڧَهُواْنِنْسَ كَمَرْ نَٻَوْنَ سُكٜىٰ؞ دَسُو يَكٜىٰ تُرٜىٰ ڧَبِيلُ، يَكُواْرٜىٰسُ حَرْ إِيَاكَرْ دُونِيَا؞ حَكَ دُبُنْ دُبَّيْ نَ إِڢْرَيِمْ سُكٜىٰ، حَكَكُمَ دُبَّنْ مَنَسّٜىٰ ذَاسُ ذَمَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Darajarsa kamar ta ɗan farin bijimi take, Ƙahoninsa kamar na ɓauna suke, Da su yake tunkwiyin mutane, Zai tura su zuwa ƙurewar duniya, Haka fa rundunan Ifraimu za su zama, Haka kuma dubban Manassa za su zama.”