Deuteronomy 4:34 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwai wani allahn da ya taɓa yin ƙoƙari yă ɗauko wa kansa wata al’umma daga wata al’umma, ta wurin gwaje-gwaje, ta wurin alamu masu banmamaki da al’ajabai, ta wurin yaƙi, ta wurin hannu mai iko, da kuma hannu mai ƙarfi, ko kuwa ta wurin ayyuka masu bangirma da na banmamaki, kamar dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi saboda ku a Masar, a kan idanunku?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ أَݣَويْ وَنِ اللَّهْ وَنْدَ يَتَٻَ ڧُواْڧَرِنْ طَوْكُواْ وَكَنْسَ وَتَ أَلْعُمَّ دَغَ ثِكِنْ ڟَكِيَرْ وَتَ أَلْعُمَّ كَمَرْ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَيِ مُكُ عَڧَسَرْ مَصَرْ؟ أَغَبَنْ عِدَنُونْكُ تَوُرِنْ حَنُّنْسَ مَيْ إِيكُواْ دَ أَيُّكَنْ بَنْ مَامَاكِ يَكَٰوُاْ بَلَعِ دَ عَلَمُ دَ أَيُّكَنْ مَاسُ بَنْ ڟُواْرُواْ دَ يَڧُواْڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ko kuma, da akwai wani allah wanda ya taɓa ƙoƙarin fitar da al'umma saboda kansa daga cikin tsakiyar wata al'umma ta wurin wahalai, da alamu, da mu'ujizai, da yaƙi, da nuna iko, da babbar razana kamar yadda Ubangiji Allahnku ya yi dominku a ƙasar Masar a kan idonku duka?