Deuteronomy 4:37 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Domin ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓi zuriyarsu a bayansu, ya fitar da ku daga Masar ta wurin kasancewarsa da kuma ƙarfinsa mai girma,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ يَڧَوْنَثِ كَاكَنِّنْكُ، شِے يَسَا يَذَاٻٜىٰكُ ذُرِيَرْسُ عَبَايَنْسُ؞ شِے دَ كَنْسَ يَڢِتَرْ دَكُو دَغَ ڧَسَرْ مَصَرْ تَوُرِنْ إِيكُوانْسَ مَيْغِرْمَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda ya ƙaunaci kakanninku shi ya sa ya zaɓi zuriyarsu a bayansu, shi kansa kuma ya fisshe ku daga Masar da ikonsa mai girma.