Deuteronomy 6:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da Ubangiji Allahnku ya kawo ku cikin ƙasar da ya rantse ga kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, yă ba ku, ƙasa mai girma, mai manyan biranen da ba ku kuka gina ba,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْكُ يَرَنْڟٜىٰوَ كَاكَنِّنْكُ، وَتُواْ إِبْرَٰهِيمْ دَ إِسْحَٰڧَ دَ يَعْڧُوبَ، ثٜىٰوَ ذَيْبَاكُ ڧَسَرْدَ ذَيْ كَيْكُ؞ وَنَّنْ ڧَسَاثٜىٰ مَيْ مَنْيَنْ بِرَنٜىٰ مَاسُ ݣَوْ وَطَنْدَ بَ كُونٜىٰ كُكَ غِنَابَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku ƙasar da ya rantse wa kakanninku Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zai ba ku manyan birane masu kyau waɗanda ba ku ne kuka gina ba,