Deuteronomy 7:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai ƙaunace ku, yă albarkace ku, yă kuma ƙara yawanku. Zai albarkaci ’ya’yanku, amfanin gonarku; hatsinku, sabon ruwan inabinku da kuma mai, ƙanana shanunku, da ’yan tumaki na tumakinku, a ƙasar da ya rantse wa kakanninku cewa zai ba ku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْ ڧَوْنَثٜىٰكُ، يَكُمَ أَلْبَرْكَثٜىٰكُ، يَكُمَ ڧَارَ يَوَنْكُ؞ ذَيْ كُوَ سَا وَیَیَنْكُ أَلْبَرْكَ، يَسَاوَ أَمْڢَانِنْ غُواْنَكِنْكُ أَلْبَرْكَ دَ حَڟِنْكُ دَ إِنَبِنْكُ دَ مَنْكُ دَ یَیَنْ غَرْكٜىٰنْكُ نَتُمَكِ دَ نَأَوَكِ دَ نَشَانُو عَثِكِنْ ڧَسَرْدَ يَرَنْڟٜىٰوَ كَاكَنِّنْكُ ذَيْبَاكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji zai ƙaunace ku, ya sa muku albarka, ya riɓaɓɓanya ku. Zai sa wa 'ya'yanku albarka, ya yalwata amfanin gonarku, da hatsinku, da inabinku, da manku, da garken shanunku, da 'yan ƙananan garkenku a ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku.