Deuteronomy 7:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ga abin da za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza keɓaɓɓun duwatsunsu, ku farfashe ginshiƙan Asheransu, ku kuma ƙona gumakansu da wuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا غَا يَدَّ ذَاكُيِ دَسُو؞ ذَاكُ رُرُّشٜىٰ بَغَدَنْسُ، كُڢَرْڢَشٜىٰ دُووَڟُنْ سُجَّدَرْسُ، كُسَسَّرٜىٰ غُمَكَنْ أَشٜىٰرَ نَاسُ، كُكُمَ ڧُواْنٜىٰ غُمَكَنْ أَلُّواْلِنْسُ دَ وُتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga yadda za ku yi da su, za ku rurrushe bagadansu, ku ragargaza al'amudansu, ku sassare ginshiƙansu na tsafi, ku ƙaƙƙone sassaƙaƙƙun siffofinsu.