Deuteronomy 9:12 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Ubangiji ya faɗa mini, “Sauka daga nan da sauri, domin mutanenka waɗanda ka fitar da su daga Masar sun lalace. Sun juye da sauri daga abin da na umarce su, suka kuma yi zubin gunki wa kansu.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَعَنً يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ مِنِ، ‹تَاشِ، كَغَنْ‌غَرُواْ دَ سَوْرِ دَغَ نَنْ، غَمَا مُتَنٜىٰنْكَ وَطَنْدَ كَڢِتَرْ دَسُو دَغَ مَصَرْ سُنْ عَيْكَتَ أَبِنْ ڧَظَنْتَا؞ سُنْيِ سَوْرِنْ كَوْثٜىٰوَ دَغَ حَنْيَرْدَ نَعُمَرْثٜىٰسُ سُبِے؞ سُنْيِ وَكَنْسُ ظُبِنْ غُنْكِنْ ڧَرْڢٜىٰ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sa'an nan ya ce mini, ‘Tashi, ka gangara da sauri, gama jama'arka wadda ka fito da ita daga Masar ta aikata mugunta, ta kauce da sauri daga hanyar da na umarce ta ta bi. Ta yi wa kanta gunki na zubi.’