Deuteronomy 9:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na ji tsoron fushi da hasalar Ubangiji, gama ya yi fushin da ku da ya isa yă hallaka ku. Amma na yi roƙo a lokacin, Ubangiji kuwa ya saurare ni.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا نَاجِڟُواْرُوانْ ذَاڢِنْ ڢُشِے دَ رَشِنْ جِنْ دَاطِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ عَكَنْكُ، حَرْ يَيِ نِيَّرْ هَلَكَاكُ؞ عَمَّا نَيِ ضُواْڧُواْ، يَهْوٜىٰهْ كُمَ يَجِنِ أَ لُواْكَثِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu'ata a wannan lokaci.