Deuteronomy 9:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In ba haka ba, ƙasar da ka fitar da mu, za tă ce, ‘Domin Ubangiji bai iya kai su cikin ƙasar da ya yi musu alkawari ba ne, kuma domin ya ƙi su, shi ya sa ya fitar da su ya kashe su a hamada.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ كَدَ مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْدَ كَڢِتَرْ دَمُو دَغَ ثِكِنْسُ سُثٜىٰ «أَيْ، سَبُواْدَ يَهْوٜىٰهْ بَيْ عِيَ كَيْسُ ثِكِنْ ڧَسَرْدَ يَيِ مُسُ أَلْڧَوَرِبَ، كُمَ سَبُواْدَ يَڧِ سُونٜىٰ، شِے يَسَا يَڢِتَرْ دَسُو دُواْمِنْ يَكَكَّشٜىٰسُ عَثِكِنْ دَاجِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Don kada mutanen ƙasar da ka fito da mu su ce, “Ai, saboda Ubangiji ya kāsa ya kai su ƙasar da ya alkawarta musu, saboda kuma ba ya ƙaunarsu, shi ya sa ya fito da su don ya kashe su a jeji.”