Ecclesiastes 10:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma kuɗi ne amsar kome.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَنْ شِرْيَ بِكِ دُواْمِنْ جِنْ دَاطِے، ضُوً إِنَبِے كُوَ دُواْمِنْ ڢَرَنْتَ رَيْ، كُطِ كُمَ دُواْمِنْ بِيَنْ كُواْوَنٜىٰ إِرِنْ بُڧَاتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma ba za ka sami ko ɗaya ba, sai idan kana da kuɗi.