Ecclesiastes 10:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne, ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne, gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka, tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَدَ كَذَاغِ سَرْكِے كُواْ عَثِكِنْ ذُوثِيَارْكَ، كَدَ كُمَ كَذَاغِ مَيْ أَرْزِڧِ كُواْ أَطَاكِنْ ݣُونْثِيَرْكَ، غَمَا وَنِ ڟُنْڟُ ذَيْ عِيَ كَيْ مَغَنَرْكَ، كُواْ وَتَ حَلِتَّ مَيْ ڢِكَڢِكَيْ ذَاتَ تُواْنَ أَسِيرِنْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kada ka zagi sarki ko a cikin zuciyarka, kada kuma ka zagi mawadaci a cikin ɗakin kwananka, gama tsuntsu zai kai maganarka, wani taliki mai fikafikai zai tone asirinka.