Ecclesiastes 2:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na yi tunani a zuciyata, “Ƙaddarar wawa za tă same ni ni ma. Wace riba ce hikimata za tă jawo mini?” Na ce a zuciyata, “Wannan ma ba shi da amfani.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْنَثٜىٰ وَكَيْنَ، «أَبِنْدَ يَڢَرُ دَ وَاوَا، ذَيْ ڢَرُ دَ نِے مَا؞ تُواْ، وَنٜىٰ أَمْڢَانِ نٜىٰ نَسَامُ نَذَمَنْ مَيْ حِكِمَ؟» سَيْنَثٜىٰ وَكَيْنَ «وَنَّنْ مَا دُكْ بَنْظَنٜىٰ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A zuciyata na ce, “Abin da yakan sami wawa shi ne kuma zai same ni. To, wace riba na ci ke nan saboda hikimar da nake da ita?” Na kuma ce a zuciyata, “Wannan ma aikin banza ne.”