Ecclesiastes 2:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَ يَسَنِ كُواْ شِے وَنْدَ ذَيْ غَاجٜىٰنِ مَيْ حِكِمَ نٜىٰ كُواْ كُمَ وَاوَا نٜىٰ؟ دُكْدَهَكَ، ذَيْ غَاجِ دُكَنْ أَمْڢَانِنْ عَيْكِنْدَ نَشَا وَهَلَرْ تَرَوَ أَ رَايُوَرْ دُونِيَرْ نَنْ؞ وَنَّنْ مَا دُكْ بَنْظَنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wa ya sani ko shi mai hikima ne, ko kuma wawa ne? Duk da haka shi zai mallaki dukan abin da na sha wahalar tanadinsa. Dukan aikin da na yi na hikima a wannan duniya aikin banza ne.