Ecclesiastes 2:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Na yi ƙoƙari in sa raina yă yi farin ciki da ruwan inabi, in kuma rungumi wauta, hankalina kuma yana yin mini jagora da hikima. Na so in ga abin da yake da daraja ga mutane a duniya a ’yan kwanakinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَيِ بِنْثِكٜىٰ عَثِكِنْ رَيْنَ، يَدَّ ذَنْبَا جِكِينَ جِنْ دَاطِے دَ ضُوً إِنَبِے، سَعَدَّ حِكِمَ تَكٜىٰبِدَ تُنَانِنَ؞ نَاكُوَ ضُنْغُمِ وَوَنْثِ دُواْمِنْ إِنْ غَا أَبِنْدَ يَكٜىٰ دَݣَوْ وَنْدَ یَنْ أَدَمْ ذَاسُيِ عَڧَرْڧَشِنْ سَمَ ثِكِنْ دُكَنْ یَنْ ݣُونَكِنْ رَايُوَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Muradina shi ne in san hikima in nemi yadda zan ji wa raina daɗi da ruwan inabi, in sa kaina ga aikata wawanci. Bisa ga tsammanina mai yiwuwa ne wannan shi ne abu mafi kyau da mutane za su yi a duniya, a 'yan kwanakinsu.