Ecclesiastes 3:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka na ga babu abin da ya fi kyau wa mutum fiye da yă more wahalar aikinsa, domin wannan ne rabonsa. Gama wa zai kawo shi yă ga abin da zai faru a bayansa?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَكُوَ غَانٜىٰ بَابُ أَبِنْدَ يَڢِ حَكَ، یَنْ أَدَمْ سُجِ دَاطِنْ عَيْكِنْسُ، غَمَا وَنَّنْ رَبُوانْ دَ اللَّهْ يَشِرْيَ مُسُنٜىٰ؞ وَنٜىٰنٜىٰ ذَيْسَا سُغَ أَبِنْدَ ذَيْ ڢَرُ بَايَنْ مُتُوَرْسُ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na gane abin da ya fi wa mutum, shi ne ya more wahalar aikinsa, gama ba wani abu da zai iya yi. Ba wata hanya da zai san abin da zai faru bayan mutuwarsa.