Ecclesiastes 4:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwai wani mutum shi kaɗai; bai shi da ɗa ko ɗan’uwa. Ba shi da hutu daga wahalarsa, duk da haka bai ƙoshi da dukiyarsa ba. Ya tambayi kansa, “Ma wane ne nake wannan wahala, kuma me ya sa nake hana kaina jin daɗi?” Wannan ma ba shi da amfani, harkar baƙin cikin ne kawai!
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْغَا وَنِ شِ كَطَيْ، بَابُ طَا، بَابُ طَنْعُوَ، دُكْدَهَكَ يَنَ تَڢَامَرْ عَيْكِ كُلُّمْ؞ بَيْ تَٻَ ڧُواْشِ دَ دُوكِيَرْسَبَ، سَيْ يَتَمْبَيٜىٰ كَنْسَ يَثٜىٰ، «غَ وَنٜىٰنٜىٰ نَكٜىٰ ڢَامَرْ عَيْكِ، حَرْ نَحَنَ وَكَيْنَ جِنْ دَاطِے؟» وَنَّنْ مَا بَنْظَنٜىٰ، ذَمَنْ بَڧِنْ ثِكِنٜىٰ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
mutumin da ba shi da kowa, ba ɗa, ba ɗan'uwa, duk da haka a kullum yana ta fama da aiki. Bai taɓa ƙoshi da wadatar da yake da ita ba. Saboda me yana ta fama da aiki, ya hana wa kansa jin daɗi? Wannan ma aikin banza ne, zaman baƙin cikin ne.