Ecclesiastes 5:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka lura da matakanka sa’ad da ka tafi gidan Allah. Ka je kusa don ka saurara a maimakon miƙa hadaya kamar wawaye, waɗanda ba su san sun yi laifi ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُورَ دَ تَڢِيَرْكَ لُواْكَثِنْ دَ كَكٜىٰ شِغَ غِدَنْ اللَّهْ ؞ ڠُومَّ كَتَڢِے دَ نِيَّرْ كَسَ كُنّٜىٰ دَاعَثٜىٰ كَتَڢِے مِيڧَ هَدَايَ إِرِ تَوَاوَايٜىٰ، غَمَا وَوَيٜىٰ بَسُ سَنْ أَبُ مَيْݣَوْ دَ مَرَرْ ݣَوْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ka yi hankali lokacin da kake shiga Haikali. Gara ka tafi can da niyyar koyon wani abu, da ka miƙa hadaya kamar waɗansu wawaye da ba su san halal da haram ba.