Ecclesiastes 5:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan na gane cewa abu mai kyau ne, daidai ne kuma mutum yă ci, yă sha, yă kuma ji daɗin aikin da ya yi a ’yan kwanakin da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum daga faman wahalarsa a duniya a cikin ’yan kwanakin da Allah ya ba shi a duniya, gama wannan shi ne rabonsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا أَبِنْدَ نَغَانٜىٰ؞ يَنَ دَݣَوْ مُتُمْ يَثِ يَشَا، يَكُمَ جِ دَاطِنْ دُكَنْ عَيْكِنْسَ أَ رَايُوَرْ دُونِيَرْ نَنْ نَیَنْ ݣُونَكِنْ دَ اللَّهْ يَبَا شِ، غَمَا وَنَّنْ رَبُوانْ دَ اللَّهْ يَشِرْيَ وَمُتُمْ نٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga abin da na gani yana da kyau, ya kuma dace, shi ne kurum mutum ya ci, ya sha, ya ji daɗin aikin da ya yi a 'yan kwanakin rai da Allah ya ba shi, gama wannan shi aka ƙaddara wa mutum.