Ecclesiastes 6:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk abin da ya kasance, to, yana da suna, kuma duk abin da mutum yake, an riga an sani. Ba mutumin da zai iya ƙarawa da wanda ya fi shi ƙarfi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ أَبِنْدَ يَكَسَنْثٜىٰ، أَنْرِغَا أَنْبَاشِ سُونَ؞ يَدَّ مُتُمْ يَكٜىٰ، أَنْرِغَا أَنْسَنِ؞ بَا مَيْ عِيَ مُسُو دَ وَنْدَ يَڢِ ڧَرْڢِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowane abu da ya kasance, an riga an ba shi suna, yadda aka yi mutum haka zai zama. Ba kuwa zai iya gardama da abin da ya fi ƙarfinsa ba.