Ecclesiastes 7:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki, amma sa’ad da suka lalace, ka tuna, Allah ne ya yi wancan shi ne kuma ya yi wannan. Saboda haka, mutum ba zai san wani abu game da nan gabansa ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَݣُونَكِنْ جِنْ دَاطِے، كَيِ مُرْنَ، عَݣُونَكِنْ وَهَلَ كُمَ، كَلُورَ، اللَّهْ نٜىٰ يَيِسُ دُكَ بِيُنْ، تَهَكَ طَنْ أَدَمْ ذَيْ غَانٜىٰ بَذَيْ سَنْ أَبِنْدَ ذَيْ ڢَرُ نَنْ غَبَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
In kana jin daɗi, ka yi murna, In kuma wahala kake sha, ka tuna, Allah ne ya yi duka biyunsa, Don kada mutum ya san abin da zai faru a nan gaba.