Ecclesiastes 7:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dukan waɗannan na gwada su ta wurin hikima na kuma ce, “Na ƙudurta in zama mai hikima,” amma abin ya fi ƙarfina.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَيِ أَمْڢَانِ دَ حِكِمَتَ دُواْمِنْ إِنْ ڠُودَ دُكَنْ وَطَنَّنْ، نَثٜىٰ، «نَيِ نِيَّ إِنْ ذَمَ مَيْ حِكِمَ،» عَمَّا أَبِنْ يَڢِ ڧَرْڢِينَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na yi amfani da hikimata don in jarraba wannan duka, domin na ɗaura aniya in zama mai hikima, amma abin ya fi ƙarfina.