Ecclesiastes 9:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na yi tunani a kan wannan na kuma gane cewa masu adalci da masu hikima da kuma abubuwan da suke yi suna a hannun Allah ne, amma ba wanda ya san ko ƙauna ko ƙiyayya ce take jiransa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِ، نَا دَطٜىٰ إِنَ تُنَانِنْ وَنَّنْ أَ ذُوثِيَاتَ ڨُورَيْ، نَا كُوَ بِنْثِكَ دُكَنْ وَنَّنْ؞ نَاغَ يَدَّ مَاسُ أَدَلْثِے دَ مَاسُ حِكِمَ دَ دُكَنْ أَيُّكَنْسُ سُنَ ثِكِنْ حَنُّنْ اللَّهْ ، حَرْ دَ ڧَوْنَرْسُ دَ ڧِيَيَّرْسُ؞ بَاوَنْدَ يَسَنْ أَبِنْدَ ذَيْ ڢَرُ دَسُو نَنْ غَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Na daɗe ina tunani ƙwarai a kan wannan abu duka, yadda Allah yake sarrafa ayyukan masu hikima da na adalai, har da ƙaunarsu da ƙiyayyarsu. Ba wanda ya san abin da zai faru nan gaba.