Ephesians 1:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثَنْ أَلْمَسِيحُ يَكٜىٰ مُلْكِ عَكَنْ دُكَنْ مَاسُ سَرَوْتَ دَ إِيكُواْ دَ ڧَرْڢِے دَ مُلْكِ؞ يَنَ دَ سُونَ وَنْدَ يَڢِ كُواْوَنٜىٰ سُونَنْدَ ذَاعَ بَايَرْ، بَا عَدُونِيَرْ نَنْ كَطَيْبَ، حَرْ مَا أَظَامَانِ مَيْ ذُوَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
a can a birbishin dukkan sarauta da iko, da ƙarfi, da mulki, a birbishin kowane suna da za a sa, ba ma a duniyar nan kawai ba, har ma a lahira ma.