Esther 1:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Domin halin Sarauniya zai zama sananne ga dukan mata, ta haka kuwa za su ƙasƙantar da mazansu su kuma ce, ‘Sarki Zerzes ya umarta a kawo Sarauniya Bashti a gabansa, amma ta ƙi zuwa.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَاشَكَّ مَاتَا نَوَنَّنْ مُلْكِ ذَاسُ جِلَابَرِ ثٜىٰوَ سَرَوْنِيَ بَشْتِ تَا ڧِ تَكَسَنْثٜىٰ أَغَبَنْ سَرْكِے سَعَدَّ يَكِرَتَ؞ وَنَّنْ كُوَ ذَيْسَا سُرٜىٰنَ مَذَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama za a sanar wa dukan mata abin da sarauniya ta yi, gama abin da ta yi zai sa su raina mazansu, gama za su ce, ‘Sarki Ahasurus ya umarta a kirawo masa sarauniya Bashti, amma ta ki.’