Esther 1:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bisa ga umarnin sarki, aka bar kowane baƙo yă sha yadda ya ga dama, gama sarki ya umarci dukan bayin da suke rarraba ruwan inabin su ba wa kowa abin da yake so.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ كُمَ يَرْدَ وَ كُواْوَ يَشَا يَدَّ يَكٜىٰسُواْ، بَ دُواْلٜىٰنٜىٰ يَشَا يَدَّ سَرْكِے يَكٜىٰ شَا بَ، غَمَا سَرْكِے يَبَادَ دُواْكَا غَ مَاسُ يِمَسَ حِدِمَ سُيِ وَكُواْوَ يَدَّ يَكٜىٰسُواْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka yi ta sha bisa ga doka, ba wanda aka matsa masa, gama sarki ya umarci fādawansa su yi wa kowa yadda yake so.