Esther 10:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mordekai mutumin Yahuda, shi ne na biyu a matsayi bayan Sarki Zerzes, mai farin ciki kuma a cikin Yahudawa, aka kuma ɗauke shi da martaba cikin ’yan’uwansa Yahudawa. Gama ya yi aiki don kyautatawar mutanensa, ya kuma yi magana don a kyautata rayuwar dukan Yahudawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوارْدٜىٰكَيْ مُتُمِنْ يَهُودَ، يَذَمَ مَتَيْمَكِنْ سَرْكِے أَهَسُرُسْ؞ مُوارْدٜىٰكَيْ يَسَامِ طَوْكَكَ دَ كُمَ ڢَضٍ جِنِ عَثِكِنْ یَنْعُوَنْسَ يَهُودَاوَا، غَمَا يَا نٜىٰمِ لَاڢِيَرْ مُتَنٜىٰنْسَ، شِينٜىٰ كُمَ يَنَ مَغَنَ أَمَدَدِنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gama sarki Ahasurus kaɗai yake gaba da Mordekai Bayahude, Mordekai kuma yana da girma a wurin Yahudawa, yana kuma da farin jini a wurin taron jama'ar 'yan'uwansa, gama ya nemi lafiyar jama'arsa, yana kuma maganar alheri ga dukan mutane.