Esther 2:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga baya sa’ad da fushin Sarki Zerzes ya huce, sai ya tuna da Bashti da abin da ta yi, da kuma dokar da ya bayar game da ita.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ وَطَنَّنْ أَبُبُوَنْ سَعَدَّ سَرْكِے أَهَسُرُسْ يَهُوثٜىٰ دَغَ ڢُشِنْسَ، سَيْ يَيِ تُنَانِ غَمٜىٰدَ بَشْتِ دَ إِرِنْ أَبِنْدَ تَيِ دَ كُمَ إِرِنْ دُواْكَرْ دَ عَكَيِ عَكَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta.