Esther 2:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kafin a kai kowace yarinya wurin Sarki Zerzes, sai ta gama watanni goma sha biyu cif ana yin mata kwalliyar da aka tsara, akan ɗauki watanni shida ana shafa mata man mur, a ɗauki watanni shida kuma ana shafa mata man ƙanshi da kayan shafe-shafe.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاڢِنْ عَكَيْ كُواْوَثٜىٰ يَارِنْيَ وُرِنْ سَرْكِے أَهَسُرُسْ، بِسَغَ ڧَٰعِدَ عَكَنْ طَوْكِ شٜىٰكَرَا غُدَا ثِڢْ أَنَڠَرَنْ جِكِنْتَ؞ عَكَنْ طَوْكِ وَتَا شِدَ أَنَ شَاڢَ مَتَ مَنْ مُرْ، أَطَوْكِ وَتَا شِدَ كُمَ أَنَ شَڢَامَتَ مَنْ ڧَنْشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da lokacin kowace budurwa ya yi da za ta shiga wurin sarki Ahasurus, bayan da ta riga ta yi wata goma sha biyu na ka'idar yin kwalliyar mata, wato takan shafe jiki da man ƙanshi wata shida, ta kuma shafe jiki da turare da man shafawa wata shida,