Esther 2:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da yamma za tă tafi can, da safe kuma ta dawo wani ɓangaren gidan matan kullen da yake a ƙarƙashin kulawar Sha’ashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwarƙwarai. Ba ta dawowa wurin sarki sai in ta gamshe shi, sai ya kuma kira ta da suna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاتَتَڢِے غِدَنْ سَرْكِے دَ يَمَّ تَكُواْمَ دَ سَڢٜىٰ ذُوَا وَنِ غِدَنْ دَ عَكٜىٰ أَجِيٜىٰ مَتَنْ سَرْكِے، وَنْدَ يَكٜىٰ أَ حَنُّنْ شَعَشْغَظْ، بَابَا نَسَرْكِے، مَيْ لُورَ دَ یَنْ مَاتَانْدَ سَرْكِے يَكٜىٰ ݣُونَ دَسُو؞ بَذَاتَ سَاكٜىٰ ذُوَا وُرِنْ سَرْكِے بَ كُمَ، سَيْدَيْ كُواْ تَغَمْشٜىٰشِ سُواْسَيْ، شِے كُمَ يَكِرَتَ دَ سُونَنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Takan tafi da yamma, ta koma gidan matan kulle na biyu da safe, a hannun Shawashgaz, bābā na sarki, wanda yake lura da ƙwaraƙwarai. Ba za ta ƙara zuwa wurin sarki ba, sai ko ta sami farin jini a wurin sarki sa'an nan a kirawo ta.