Esther 2:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da lokaci ya yi da Esta (yarinyar da Mordekai ya ɗauka tamƙar ’yarsa, ’yar kawunsa Abihayil) za tă shiga wurin sarki, ba tă nemi a ba ta kome ba in ban da abin da Hegai, bābān sarki mai lura da gidan matan kulle, ya ba da shawara. Esta kuwa ta sami tagomashin kowa da ya ganta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
لُواْكَثِ يَيِ دَ عٜىٰسْتَا ذَاتَ شِغَ وُرِنْ سَرْكِے؞ وَنَّنْ عٜىٰسْتَا عِتَثٜىٰ یَرْ أَبِهَيِلْ طَنْعُوَنْ بَابَنْ مُوارْدٜىٰكَيْ، وَدَّ مُوارْدٜىٰكَيْ يَطَوْكٜىٰتَ تَذَمَ یَرْسَ؞ أَ لُواْكَثِنْ كُوَ عٜىٰسْتَا بَتَاضُواْڧِ كُواْمٜىٰبَ، سَيْدَيْ تَابِے شَوَرَرْ هٜىٰغَيْ بَابَا نَسَرْكِے مَيْ لُورَ دَ غِدَنْ دَ عَكٜىٰ أَجِيٜىٰ مَتَنْ سَرْكِے؞ عٜىٰسْتَا كُوَ تَنَدَ ڢَضٍ جِنِ أَعِدُوانْ كُواْوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da lokacin Esta 'yar Abihail, kawun Mordekai, wadda Mordekai ya karɓe ta tankar 'yarsa, ya yi da za ta shiga wurin sarki, ba ta bukaci kome ba, sai dai abin da Hegai, bābā na sarki, wanda yake lura da mata, ya ce. Esta kuwa tana da farin jini a idon duk wanda ya gan ta.