Esther 2:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, sarki ya so Esta fiye da duk sauran matan, ta kuma sami tagomashinsa da kuma yardarsa fiye da duk sauran budurwai. Saboda haka ya sa rawanin sarauta a kanta, ya kuma mai da ita sarauniya a maimakon Bashti.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَرْكِے كُوَ يَسُواْ عٜىٰسْتَا ڢِيٜىٰدَ سَوْرَنْ مَاتَا، تَا كُوَ سَامِ أَلْحٜىٰرِ دَ ڢَضٍ جِنِ دَغَ غَرٜىٰشِ ڢِيٜىٰدَ دُكَنْ سَوْرَنْ بُدُرْوَيْ؞ سَبُواْدَ حَكَ يَسَا مَتَ هُولَرْ مُلْكِ، يَمَيْدَ عِتَ سَرَوْنِيَ أَمَيْمَكُوانْ بَشْتِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
sai sarki ya ƙaunaci Esta fiye da dukan sauran matan. Ta kuwa sami alheri da farin jini a wurinsa fiye da sauran budurwan, saboda haka ya sa kambin sarauta a kanta. Ya naɗa ta sarauniya maimakon Bashti.