Esther 2:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sarki kuwa ya yi ƙasaitacciyar liyafa, liyafar Esta, wa dukan hakimansa da shugabannin masarautarsa. Ya yi shelar hutu ko’ina a larduna, ya kuma raba kyautai a yalwace irin na sarauta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سَرْكِے كُوَ يَيِ بَبَّنْ بِكِ دُواْمِنْ يَغِرْمَمَ عٜىٰسْتَا؞ يَغَيَّثِ مَنْيَنْ مُتَنٜىٰنْسَ دَ دَتَّاوَنْسَ؞ يَكُمَ بَادَ هُوتُ غَ دُكَنْ يَنْكُنَنْ مُلْكِنْسَ؞ يَبَادَ ݣَوْتَيْ عَيَلْوَثٜىٰ بِسَغَ أَرْزِڧِنْ مُلْكِنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sarki kuwa ya yi wa sarakunansa da barorinsa ƙasaitaccen biki saboda Esta. Ya kuma ba larduna hutu, ya ba da kyautai da yawa irin na sarauta.