Esther 2:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da aka bincika labarin aka kuma iske gaskiya ne, sai aka rataye hafsoshin nan biyu a wurin rataye mai laifi. Aka rubuta dukan wannan a cikin littafin tarihi a gaban sarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ عَكَيِ بِنْثِكٜىٰ، عَكَ غَانٜىٰ ثٜىٰوَ لَابَرِنْ مُوارْدٜىٰكَيْ غَسْكِيَ نٜىٰ؞ سَيْ عَكَ رَاتَيٜىٰ وَطَنَّنْ مُتُمْ بِيُ عَكَنْ دُواْغُوانْ كَتَكُوانْ رَاتَيَ مُتَنٜىٰ؞ سَرْكِے كُوَ يَا بَادَ عُمَرْنِ عَكَ رُبُوتَ وَنَّنْ لَابَرِ عَثِكِنْ لِتَّڢِنْ تَارِيحِ نَمُلْكٍ أَغَبَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da aka bincika al'amarin aka tarar haka yake. Sai aka rataye mutum biyu ɗin a kan gumagumai. Aka kuma rubuta labarin a littafin tarihi a gaban sarki.