Esther 2:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bari sarki yă naɗa komishinoni a kowane yanki na masarautarsa, domin su kawo dukan waɗannan kyawawan ’yan mata cikin harabar mazaunin masarautar a Shusha. Bari a sa su a hannun Hegai, bābān sarki, wanda yake lura da mata, bari kuma a yi musu kulawa ta musamman.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَرِ سَرْكِے يَذَاٻِ وَكِلَيْ عَكُواْوَنٜىٰ يَنْكِ نَڧَسَرْ دُواْمِنْ سُكَٰوُاْ دُكَنْ وَطَنَّنْ ݣَوَوَنْ یَنْ مَاتَا، بُدُرْوَيْ أَغِدَنْ دَ عَكٜىٰ أَجِيٜىٰ مَتَنْ سَرْكِے أَوُرِے مَيْ كَتَنْ‌غَ عَبِرْنِنْ شُوشَنْ؞ عَبَرْسُ أَ حَنُّنْ هٜىٰغَيْ، وَنْدَ يَكٜىٰ بَابَا نَسَرْكِے مَيْ كُلَ دَ مَتَنْ سَرْكِے، يَسَا سُسَامِ كَايَنْ ڠَرَنْ جِكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bari kuma sarki ya sa shugabanni a cikin dukan lardunan mulkinsa su tara dukan kyawawan 'yan mata, budurwai, a gidan matan kulle a masarauta a Shushan, ƙarƙashin Hegai bābā na sarki, wanda yake lura da mata. A riƙa ba budurwan man shafawa.