Esther 2:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da aka yi shelar umarni da dokar sarki, sai aka kawo ’yan mata masu yawa a mazaunin masarauta a Shusha, aka kuma sa su ƙarƙashin kulawar Hegai. Aka kawo Esta ma zuwa fadar sarki, aka danƙa ta wa Hegai, wanda yake lura da mata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ عَكَيِ شٜىٰلَرْ عُمَرْنِ دَ دُواْكَرْ سَرْكِے، سَيْ عَكَ تَتَّارَ یَنْ مَاتَادَيَوَ أَ شُوشَنْ أَغِدَنْ سَرْكِے أَ حَنُّنْ هٜىٰغَيْ؞ عٜىٰسْتَا تَنَ ثِكِنْسُ، عِتَمَا عَكَ أَجِيٜىٰتَ أَغِدَنْ سَرْكِے، أَ حَنُّنْ هٜىٰغَيْ مَيْ لُورَ دَ غِدَنْ دَ عَكٜىٰ أَجِيٜىٰ مَتَنْ سَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da aka yi shelar dokar sarki, aka kuma tattara 'yan mata a masarauta a Shushan, a hannun Hegai, sai aka ɗauko Esta zuwa fādar sarki, aka sa ta a hannun Hegai wanda yake lura da mata.