Esther 3:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَبَا یَنْ كَدَتَݣُونَ وَسِيڧُنْ ذُوَاغَ كُواْوَنٜىٰ يَنْكِ نَمُلْكٍ؞ عَثِكِنْ وَسِيڧُنْ أَنْرُبُوتَ ثٜىٰوَ عَكَنْ رَانَ تَغُواْمَشَا عُكُ غَ وَتَنْ أَدَرْ، ذَاعَ هَلَّكَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ يَهُودَ، عَكَكَّشٜىٰسُ عَكُمَ كَوَرْدَسُو، مَنْيَ دَ ڧَنَانَا، مَاتَادَ يَارَا، عَكُمَ ڨُوثٜىٰ كَايَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka ba 'yankada-ta-kwana takardun zuwa dukan lardunan sarki don a hallaka Yahudawa, a karkashe, a ƙarasa su, ƙanana da manya, mata da maza, duk a rana ɗaya, wato ran goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato watan Adar, a kuma washe dukiyoyinsu.