Esther 3:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Haman ya ce wa Sarki Zerzes, “Akwai waɗansu mutanen da suke a warwatse, sun kuma bazu a cikin mutane cikin dukan lardunan masarautarka, waɗanda al’adunsu sun yi dabam da na dukan sauran mutane. Mutanen nan ba sa biyayya da dokokin sarki; ba zai yi wa sarki kyau a jure su ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ هَامَٰنَ يَثٜىٰ وَ سَرْكِے أَهَسُرُسْ «أَݣَويْ وَتَ ڧَبِيلَ أَوَرْوَڟٜىٰ عَثِكِنْ ڧَبِيلُنْ دُكَنْ يَنْكُنَنْ مُلْكِنْكَ؞ أَلْعَادَرْسُ دَبَمْ ثٜىٰ دَ نَسَوْرَنْ مُتَنٜىٰ، بَاسَ كُمَ كِيَايٜىٰ دُواْكَرْ سَرْكِے؞ دُواْمِنْ حَكَ بَيْ كَمَاتَ سَرْكِے يَيِ حَڧُرِ دَسُوبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan Haman ya ce wa sarki Ahasurus, “Akwai waɗansu mutane da suke warwatse a jama'ar dukan lardunan mulkinka. Dokokinsu sun sha bambam da na sauran mutane, ba su kuma kiyaye dokokin sarki, don haka ba shi da amfani a wurin sarki ya yi ta haƙuri da su.