Esther 5:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً عَكَنْ رَانَ تَ عُكُ، سَيْ عٜىٰسْتَا تَسَا رِيغُنَنْ مُلْكِنْتَ، تَشِغَ ذَوْرٜىٰ نَثِكِ نَغِدَنْ سَرْكِے، تَنَ ڢُسْكَنْتَرْ طَاكِنْ دَ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِ تَكٜىٰ؞ سَرْكِے كُوَ يَنَ ظَوْنٜىٰ عَكَنْ كُجٜىٰرَرْ مُلْكِنْسَ يَنَ ڢُسْكَنْتَرْ ڧُواْڢَرْ شِغَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kan rana ta uku sai Esta ta sa rigunan sarautarta, ta tafi, ta tsaya a shirayi na ciki na fādar sarki, kusa da ɗakin sarki. Sarki kuwa yana zaune a gadon sarautarsa, a gidan sarautarsa, daura da ƙofar shiga fāda.