Esther 5:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda suke shan ruwan inabi, sarki ya sāke ce wa Esta, “Yanzu, mece ce bukatarki? Za a biya miki shi. Kuma mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سُكٜىٰ ثِكِنْ شَنْ ضُوً إِنَبِے، سَيْ سَرْكِے يَتَمْبَيِ عٜىٰسْتَا يَثٜىٰ «مٜىٰكِكٜىٰ بُڧَاتَ؟ ذَاكِ سَامُ؞ مٜىٰنٜىٰنٜىٰ ضُواْڧُوانْكِ؟ كُواْ دَمَا رَبِنْ مُلْكِنَ نٜىٰ، ذَنْبَاكِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da suke shan ruwan inabi, sai sarki ya tambayi Esta, “Mece ce bukatarki? Za a biya miki ko da rabin mulkina ne.”